Connect with us

Labarai

Rundunar Soji Ta Kubutar Da Dalibar Chibok Da Wasu Mata Uku

Dakarun saji na Operation Hadin Kai da ke aiki a yankin Arewa maso gabas sun ceto wata ‘yar Chibok da wasu mutane uku da ‘yan ta’addar Boko Haram suka sace shekaru takwas da suka gabata.

A watan Afrilun 2014 ne ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi garkuwa da dalibai mata 276 yawancinsu Kiristoci ‘yan shekara 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ‘yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno.

A wata sanarwa da rundunar soji ta fitar a ranar Asabar din nan a shafinta na Facebook, ta ce sojojin runduna ta 21 Special Armored Brigade, Sector 1 Operation HADIN KAI (OPHK) a karamar hukumar Bama ta jihar Borno ne suka ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

A’isha Grema, ‘yar Chibok, ta samu tarba daga kungiyar matan jami’an sojin Najeriya (NAOWA).

Shugabar NAOWA, Misis Salamatu Yahaya, ta bayar da gudummawar kayan agaji da tallafin kudi ga sabbin ‘yan matan Chibok da aka ceto, in ji sanarwar kungiyar.

“An ceto Aisha ne a jiya, 12 ga watan Agusta, 2022 tare da yaronta dan shekara hudu (4) ta hannun sojojin 21 Special Armored Brigade, Sector 1 Operation HADIN KAI (OPHK) a karamar hukumar Bama (LGA) yayin da sauran ‘yan matan uku rundunar bataliya ta 242, Sector 3 OPHK a karamar hukumar Mongonu ta jihar Borno ta ceto su,” in ji sanarwar.

CHANNELS TV

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet