Labarai
Nasarawa: Ƴan sanda sun tabbatar da sace kwamishinan yaɗa labarai

Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, ta tabbatar da rahoton da ke cewa ƴan bindiga sun sace kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar na jihar Yakubu Lawal.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Ramhan Nansel, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Talata a Lafia babban birnin jihar.
Ya ce, Ƴan sanda sun kai ɗauki gidan kwamishinan dai-dai lokacin da ƴan bindigar ke ta harbe-harbe.
Ya ƙara da cewa, “yanzu haka ana ci gaba da bincike da Kuma ƙoƙarin ceto Kwamishinan da sauran waɗanda lamarin ya shafa daga hannun ƴan bindigar.
karkashin jagorancin kwamandan yankin Akwanga, ACP Halliru Aliyu.”
Haka kuma ya ce, kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umarnin cewa duk wanda ke da bayanan da zasu taimaka wa hukumar wajen ceto wanda aka sace tare da kama masu garkuwa da mutanen to ƙofa a buɗe take.
Haka kuma rundunar ƴan sandan jihar ta Nasarawa ta ƙara da cewa duk wanda ke da wani bayani zai iya tuntubar rundunar ta lambobi kamar haka: 08035951018, 08033806409, 08037461715 da kuma 08036157659.