Ilimi
Kungiyoyin NASU Da SSANU Sun Dakatar Da Yajin Aikin Da Suke Yi

Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in ta kasa (SSANU) da kungiyar ma’aikatan da ba malamai ba ta NASU a ranar Asabar din nan sun dakatar da yajin aikin da suke yi bayan wata ‘yar gajeriyar ganawa da ministan ilimi, Adamu Adamu a Abuja.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Ana sa ran dai dakatarwar za ta fara aiki daga ranar Larabar mako mai zuwa.
A cewar Ministan Ilimi, Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 50 don biyan alawus-alawus ga mambobin SSANU, NASU da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i.