Labarai
Gwamnan Gombe ya miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar sarkin Funakaye

Gamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana mutuwar marigayi sarkin Funakaye marigayi Alhaji Muazu Muhammad Kwairanga III a matsayin babban rashi ga masarautarsa har ma da jihar da kuma Najeriya baki ɗaya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran gwamnatin jihar.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ta cikin sanarwar ya ce, jihar Gombe ta yi rashin sarki jajirtacce musamman wajen ayyukan ci gaba da kuma tabbatar da haɗin kai da haɓɓaka ci gaban al’umma.
Haka kuma ta cikin sanarwar, Gwamnan ya miƙa ta’azziyarsa ga iyalan sarkin da masarautar Funakaye baki ɗaya.