Siyasa
Sai mun ƙwace mulkin Borno daga hannun Zulum- Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa za ta ƙwace mulkin jihar Borno daga hannun gwamnan ta Farfesa Babagana Umara Zulum a zaɓen baɗi.
Rahotonni sun bayyana cewa Kwankwaso ya furta hakan ne a Maiduguri babban birnin jihar yayin bude ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a jiya Asabar.
Haka kuma Kwankwaso ya ƙara da cewa, jam’iyyar NNPP ce za ta lashe zaɓuka a dukkan matakai tun daga na jihohi har ma da Tarayya.
Ya kuma buƙaci magoya bayansa da su kasa su tsare a zaɓen na baɗi domin tabbatar da samun nasarar jam’iyyar ta NNPP.