Sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa Malam Ibrahim Shekarau, ya sanar da ficewar sa da ga jam’iyar NNPP zuwa PDP.
Malam Shekarau ya sanar da ficewar tasa ne a wani taro da ya gudanar a gidansa da ke unguwar Munduɓawa da ke Jihar Kano a yau Litinin.
Ya ce tuni ya rubuta wasika zuwa ga uwar jam’iyyar NNPP ta ƙasa, da matakin jiha, Ƙaramar Hukuma da Mazaɓa cewa ya fice da ga jam’iyar.
Ya kuma ƙara da cewa ya rubuta wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da matakin jiha cewa ya ajiye takararsa ta sanata a jam’iyar NNPP.
Shekarau ya ƙara da cewa zai iya barin jam’iyya ko sau ɗari ne matuƙar za a riƙa yin rashin adalci da zalunci a jam’iyya.
Taro sauya sheƙar tasa ya samu halastar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen baɗi Alhaji Atiku Abubakar, da wanda zai yi masa mataimaki Daniel Okowa da Gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da sauran manya da masu ruwa da tsaki na jam’iyar PDP.