Labarai
Babbar kotun tarayya ta sake ƙin amincewa da buƙatar belin Abba Kyari

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sake ƙin amincewa da buƙatar Abba dakataccen mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyari, da wasu mutane huɗu na sanya su a hannun beli.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Alƙalin kotun mai shari’a Emeka Nwite, ne ya sanar da ƙin amincewar kotun yayin zamanta na yau Talata.
Mai shari’a Emeka Nwite, ya ce waɗanda ake zargin sun gaza gabatar da gamsassun hujjoji da za su sanya kotun ta amince da buƙatar bada su beli.
Haka kuma ya ƙara da cewa don haka ya sake tabbatar da hukuncin farko da kotu ta yanke a ranar 28 ga watan Maris ɗin bana.