Labarai
Sarki Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar jaje kasuwar Beirut

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajantawa ƴan kasuwar sayar da wayoyin hannu ta Beirut sakamakon ibtula’in da ya faru na rugujewar wani Gini.
Sarkin ya furta hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga al’ummar kasuwar da mutanan jihar Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero,ya kuma yi Kira da injiniyoyi da su riƙa mayar da hankali wajen bada shawarwarin yin gine-gine masu inganci.
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ƙara da bai wa ƴan kasuwar haƙuri bisa faruwar iftila’in yana mai cewa muƙaddari ne daga Allah maɗaukakin sarki.
Haka kuma ya yi fatan Allah ya bai wa waɗanda suka raunata lafiya ya kuma jiƙan waɗanda suka rasu.