Labarai
APC ta naɗa Bala Ibrahim a matsayin sabon Daraktan yaɗa labaranta

Jam’iyyar APC ta sanar da naɗa Malam Bala Ibrahim a matsayin daraktanta na yaɗa labarai na ƙasa.
Hakan dai na cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore ya sanyawa hannu tare da yaɗa ta a daren yau Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa naɗin na Malam Bala Ibrahim a matsayin ya fara aiki ne daga yau Alhamis 1 ga watan Satumba.
Sanarwar ta kuma taya murna tare da jan hankali ga sabon Daraktan da cewa, ”Yayin da muke taya ka murna kan nadin da akayi maka, muna fatan za ka bada taka gudun-mawar ta hanyar gudanar da ayyukanka cikin nasara da kwanciyar hankali”.
Malam Bala Ibrahim, dai ɗan asalin jihar Kano ne kuma gogaggen ɗan jarida kuma ƙwararren kana mai sharhi akan al’amuran yau da kullum.