Connect with us

Labarai

Kano: Jami’an KAROTA sun sake cafke babbar mota maƙare da Barasa

A karo na biyu cikin ƙasa da mako guda, Hukumar kula da zirga-zirga ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta sake cafke babbar motar ɗaukar kaya a maƙare da Barasa.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na hukumar Malam Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar a yau Alhamis.

Sanarwar ta ce, Hukumar ta sami nasarar cafke motar ƙirar Tirela ne a kan titin Bello Dandago da misalin ƙarfe 2:30 na daren jiya Laraba a ƙoƙarin direban motar na shiga cikin unguwar Sabon Gari.

Haka kuma ya ce, Jami’an KAROTA sun cafke motar dai-dai lokacin da suka buƙaci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar abinda ya ɗakko watau Way bill, inda ya bayyana musu cewa Kwalaye kawai ya ɗakko
Bayan da jami’an suka matsa bincike sai suka tabbatar da Giya ce a cikin babbar motar.

Shugaban Hukumar KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya bayyana cewa Hukumar KAROTA ba za ta gajiya ba wajen kama duk wani nau’in kayan da aka ci garo da su wanda dokar jihar Kano bata amince a shigo da su ba
Ya ƙara da cewa za a ƙara baza jami’an KAROTA musamman kan manyan titinan jihar nan domin ganin an daƙile shigowar kayayyakin da dokar jihar Kano ta haramta.

Sanarwa ta kuma bayyana cewa m, an cafke motar ne ƙasa da mako guda da hukumar ta cafke manyan motocin Tirela guda biyu maƙare da Barasa wadda adadinta ya kai fiye da Kwalba dubu arba’in da kuɗinta ya haura naira miliyan arba’in.

Haka kuma ta cikin sanarwar, Hukumar ta KAROTA ta ce za ta miƙa barasar ga hukumar Hisbah da zarar ta kammala bincike domin ɗaukar mataki na gaba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet