Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Tallafawa Mutane 6000 Da Kudi A Jihar Katsina

Gwamnatin tarayya ta tallafawa akalla mutane 6,000 da suka karbi Naira 20,000 kowannensu a matsayin tallafin kudi a jihar Katsina a wani bangare na kokarin gwamnatin tarayya na rage radadin talauci a tsakanin talakawa da marasa galihu a kasar nan.

Hakazalika, sama da iyalai 1,000 a jihar ne suka ci gajiyar abinci da kayan abinci a matsayin tallafin da gwamnatin tarayya ke yi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Ministar kula da jin kai da magance iftila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana hakan a unguwar Mazoji da ke Daura, yayin da ta kaddamar da rabon kayayyakin tallafin.

Kana ta ce wasu mutane 500 sun ci gajiyar aikin jinya kyauta, inda aka yi masu maganin matsalolin ciwon ido daban-daban tare da baiwa marasa lafiya da suka amfana kyauta da magunguna da sauran kayayyaki masu mahimmanci kamar gilashin ido da ke taimakawa mutum wajen gani.

Ministar ta ce gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi suna gudanar da tantance bukatu da suka shafi bala’in ambaliyar ruwa da ya rutsa da yawancin jihohin tarayyar kasar nan, da nufin tallafa wa wadanda abin ya shafa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet