Connect with us

Labarai

Wani Matashi Ya Rasa Ransa, Yayin Da Ya Je Ceto Saniya

 

Wani matashi mai Shekara 18 mai suna Adamu Musa ya mutu a kokarin ceto saniyar sa a karamar hukumar Buji ta jihar Jigawa.

Wani mazaunin garin ya shaidawa jaridar DAILY POST cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a Unguwar Magina da ke cikin garin Buji.

Ya ce wanda abin ya shafa ya rasa ransa ne a wani tafki a lokacin da yake kokarin ceto saniyarsa da ta zame ta fada ciki a lokacin da take kiwo a kewayen yankin.

Kakakin Hukumar Kula da tsaron farar hula ta  NSCDC, CSC Adamu Shehu shi ma ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin.

A cewarsa, “Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Asabar, 3 ga watan Satumba, 2022, da misalin karfe 02:00 na rana, inda matashin ya dauki shanunsa guda biyu zuwa gona, ya sako su domin ciyar da su da ciyawar da ke kusa.

“Abin takaici sai daya daga cikin shanun ta zame ta fada cikin wani tafki da ke kusa da gonar da suke kiwo.

“Da ya ga abin da ya yi muni, marigayin ya garzaya don ceto saniyarsa, amma ruwa ya nutse duk da kokarin da mutanen yankin da jami’an NSCDC suka yi na ceto shi,” inji shi.

Ya ce daga baya aka tsinci gawar mamacin ranar Lahadi da misalin karfe 01:00 na safe.

Ya ce an yi wa marigayin cikakken bincike, aka tabbatar da mutuwarsa sannan aka mika shi ga iyayensa domin su yi mashi jana’iza yadda ya kamata, yayin da aka ceto saniyar a raye.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet