Labarai
Ƴan bindiga sun sace matafiya a babbar hanyar Benin

Wasu gungun ƴan bindiga sun sace matafiya da dama a babban titin Benin zuwa garin Owo na jihar Ondo.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Haka kuma ta ƙara da cewa har kawo yau ba a kai ga gano adadin mutanen da lamarin ya ritsa da su ba.
Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa, waɗanda ƴan bindigar suka sace sun fi mutum arba’in.
Haka kuma jaridar ta ƙara da cewa, a jiya Lahadi ne jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sandan jihar Ondo SP Funmilayo Odunlami, ta ce, rundunar ba ta kai ga tantance adadin mutanen da iftila’in ya rutsa da su ba.