Labarai
Hukumar NDLEA ta cafke ƙasurguman ƴan ta’adda 8

Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA, sun cafke wasu mutane takwas a wata maɓoyar ƴan ta’adda.
Ana dai zargin mutanen da cewa suna cikin ƴan ta’addan da suka addabi al’umma musamman wajen yin garkuwa da mutane da aikata muggan laifuka a jihar Ondo.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar Mista Femi Babafemi ya fitar.
Sanarwar ta ce, Jami’an hukumar ta NDLEA sun ƙaddamar da samamen ne a maɓoyar ɓata garin bayan samun wani rahoto cewa akwai ɓata gari a cikin dajin Ala wanda ke yankin ƙaramar hukumar Akure ta Arewa a jihar ta Ondo.
Haka kuma ya ce, sun kai farmakin ne a ranar Juma’ar da ta gabata.
Sanarwar ta kuma ce, an samu nasarar ƙwato buhu ashirin da biyar na ganyen Wiwi mai nauyin kilogiram ɗari biyu da casa’in da shida da wasu abubuwan fashewa guda shida da bindigogi da harsasai guda shida da babura guda hudu da kuma layu.