Connect with us

Labarai

Mutane 9 Sun Mutu Yayin Da 10 Suka Sami Raunuka A Wani Hatsarin Mota

Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa mutane 9 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 10 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Yangoji zuwa Abaji a babban birnin tarayya, Abuja.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in kula da ilimin jama’a na Corps Bisi Kazeem, hatsarin ya rutsa da wata mota kirar Toyota Hiace Bus mai lamba KTG-450 KQ da kuma motar Howo Sino a kan hanyar Yangoji zuwa Abaji da misalin karfe 06:05 na safiyar ranar Asabar.

Ya ce motar bas din ta fito ne daga jihar Osun yayin da ta nufi jihar Katsina amma abin takaici ta daki wata tirela da ke tsaye.

Ya jaddada cewa duka motocin da hadarin ya rutsa da su, motocin kasuwanci ne.

Kazeem ya ce, “Mutane 22 ne suka yi hatsarin. Dukkansu maza ne. An jikkata 10 sannan tara suka mutu. An ba da agajin gaggawa ga mutane biyu. Hukumar FRSC ta sami Naira 3,170, da buhuna shida da kuma wayoyin hannu daban-daban guda 4.

“An ajiye gawarwakin mutane taran a wajen ajiyar gawawwaki na babban asibitin Kwali kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Kwali ta dauki nauyin gudanar da bincike.”

A cewar Kazeem, Mukaddashin Rundunar Corps Marshal, Dauda Biu, ya ce hadurran sun samo asali ne daga hatsarin da ke tattare da gudin wuce sa’a, daga bisani kuma aka rasa yadda za a shawo kan lamarin.

Biu ya lura cewa hadarurrukan da daddare sun fi kashe mutane fiye da yadda suke yi da rana.

Ya ci gaba da cewa rundunar za ta ci gaba da jan hankalin jama’a ta hanyar wayar da kan jama’a har sai an samu nasarar da ake bukata.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ya kuma bukaci masu ababen hawa da su tabbatar da cewa an tsara motocinsu kafin su dora su akan hanya domin gujewa hadurran hanyoyin musamman da daddare.

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet