Ilimi
Yajin Aikin ASUU: An Shiga Wata Ganawar Gaggawa

Ministan ilimi, Adamu Adamu, tare da masu ruwa da tsaki irin su magatakardar hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sikandire, Farfesa Ishaq Oloyede; Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Farfesa Abubakar Rasheed; Emeritus Peter Okebukola da Nimi-Briggs; tare da dukkan shugabannin jami’o’in tarayya da mataimakan shugabannin jami’o’in tarayya sun fara wani zama na musamman.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa zaman ya kasance na sirri ne, kuma zai mayar da hankali kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in take yi yanzu haka.
“Zan so in yi tambaya cikin girmamawa cewa shugabannin ‘yan jarida su yi mana uzuri domin mu fara shawarwari,” in ji Adamu Adamu.
Tun da farko dai Ministan ya koka da yadda kungiyar ASUU ta kasa janye yajin aikin da suke yi duk da tsoma bakin da gwamnati ta yi.
ASUU ta shiga yajin aikin ne a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, 2022 biyo bayan abin da kungiyar ta yi wa lakabi da gazawar gwamnati wajen biyan wasu bukatu.