Featured
Mbappe ya zura kwallaye 2 a wasan PSG na farko karkashin gasar zakarun Turai

Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Kylian Mbappe ya yi nasarar zura kwallaye 2 a wasa tsakanin Paris St-Germain da Juventus a haduwar da suka yi a wasan farko na matakin rukuni a gasar zakarun nahiyar Turai da suka tashi 2-1.
Mbappe ya zura kwallon farko a ragar Juventus ne da taimakon Neymar wanda ya kara masa kwallo jim kadan bayan ya karbo ta daga Achraf Hakimi.
Saura kiris matashin dan wasan gaban na Faransa ya ci kwallaye 3 rigis a wasan jiya, amma har sau biyu ya na kuskuren buga kwallayen zuwa can gefen fili.
Dan wasan da Juventus suka sanya daga baya, Weston McKennie ya farke musu kwallo 1, a yayin da mai tsaron ragar PSG Gianluigi Donnarumma ya kama wata kwallo da Dusan Vlahovic ya yi yunkurin antayawa da kai.
Da yiwuwar dai PSG ta shiga gasar ta bana da dukkanin karfinta a kokarin lashe kofin, duk da cewa za ta iya gamuwa da cikas tun daga matakin rukuni.