Labarai
Wani Faduwar Gini Ya Yi Sanadiyyar Rasa Rayukan Yara Uku

Yara 3 ne aka rawaito sun mutu sakamakon ruftawar gini biyo bayan samun ruwan sama da aka shafe sa’o’i ana yi a Jigawar Tsada da ke karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa.
Wadanda abin ya shafa sun hada da Farida Idi ‘yar shekara shida da Mariya Idi ‘yar shekaru uku da kuma Bilkisu Yahya ‘yar wata 18 da haihuwa duk mazauna kauyen Yakasai Jigawar Tsada.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce wadanda lamarin ya shafa sun mutu nan take.
Sanarwar ta kara da cewa, “Da samun rahoton, jami’an tsaro sun bazama zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe sauran sannan aka garzaya da su zuwa babban asibitin Dutse inda Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsu.”
Ya kara da cewa an dauki hoton gawarwakin kuma aka mika wa ‘yan uwan wadanda abin ya shafa domin yi musu jana’iza.