Featured
Allah ya yi wa ɗan Sanata Kabiru Gaya rasuwa

Allah ya yi wa ɗan gidan Sanatan mazaɓar Kano ta Kudu, Sadiq Kabiru Gaya rasuwa a yau Talata.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, mai magana da yawun Sanatan Malam Hussaini Ambo Indabawa ne ya tabbatar mata da rasuwar Sadiq wanda lauya ne.
Haka kuma jaridar ta ruwaito cewa marigayin ya rasu ne a birnin tarayya Abuja.
Solacebase ta kuma ruwaito cewa Hussaini Ambo Indabawa, ya ce, an yi jana’izar marigayin da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
Marigayi Sadiq Kabiru Gaya, ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa biyu.