Connect with us

Labarai

Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Jihohi Da Su Dauki Matakin da Ya Dace

Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta roki hukumomi a jihohi daban-daban da su jajirce wajen ganin an kiyaue kara samun ambaliyar ruwa.

Babban Daraktan hukumar NIHSA, Clement Nze, wanda ya bayar da sanarwar a wata sanarwa a ranar Juma’ar nan a Abuja, ya bukaci jihohi da su dauki matakan da suka dace don hana mummunar matsalar ambaliyar ruwa a shekaru masu zuwa.

Najeriya a cewarsa, yanzu haka tana cikin kalubalan yanayi na ambaliyar ruwa, don haka akwai bukatar gwamnati musamman a matakin jihohi da na kananan hukumomi su kara kaimi tare da daukar matakan dakile bala’o’i masu alaka a yankunansu.

Nze ya bayyana cewa kusan dukkan jahohi 36 da babban birnin tarayya Abuja sun fuskanci ambaliyar, ya yi alhinin faruwar lamarin a jihar Jigawa inda mutane sama da 72 suka mutu.

Ya yi gargadin cewa tsarin kogunan Neja da Benuwai sun fara habaka kuma Najeriya tana kan iyakar kogin Neja da kasashe tara suka mamaye.

Musamman, shugaban NIHSA ya roki hukumomi a jihohi 13 da suka hadu a manyan kogunan Neja da Benue da su samar da isassun matakan da suka dace don dakile duk wani bala’i da zai biyo baya.

Jihohin da abin ya shafa sun hada da Kebbi, Niger, Adamawa, Taraba, Benue, Nasarawa, Kogi, Edo, Delta, Anambra, Cross River, Rivers da Bayelsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet