Labarai
Kotu ta kori ƙarar Ganduje da Abduljabbar ya shigar

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta kori karar da Sheikh Abdul-jabbar Nasiru Kabara, ya shigar a gabanta ta yana ƙalubalantar gwamnatin jihar Kano da wasu mutane da suke zarginsa da yin kalaman batanci ga ma’aiki.
Alkalin kotun mai shari’a Emeka Nwite, ya yanke wannan hukunci a zaman kotun na yau Litinin.
Yayin yanke hukuncin, alƙalin ya ce, shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1201/2022 a kotun tamkar yin karan tsaye ne ga ci gaba da sauraren tuhumar da ake yi wa malamin, kasancewar akwai makamanciyar karar a babbar kotun tarayya da ke nan Kani.
Mai shari’a Emeka Nwite, ya kara da cewa, shigar wannan kara da lauyan malamin Barista Shehu Dalhatu, ya yi wani yunkuri ne na karkatar da hankali kotu dangane da shari’ar da ake yi da malamin, kuma hakan abun Al== wadai ne.
Ƙarar wadda lauyan malamin Barista, Dalhatu, ya shigar an sanya babbar kotun shari’ar addinin Musulunci da kuma gwamnatin jihar Kano a matsayin wadanda ake kara na daya da na biyu.