Labarai
Gwamnatin Jihar Yobe Za Ta Kashe Sama Da Biliyan 10 A Wasu Ayyukan Tituna

Gwamnatin jihar Yobe ta ce za ta yi amfani da Naira biliyan 10.8 daga cikin Naira biliyan 18 da gwamnatin tarayya ta mayar mata a ayyukan gina tituna.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa dawo da Naira biliyan 18 na baya-bayan nan ya shafi biyan kudin wasu manyan tituna biyar da jihar ta gina a madadin gwamnatin tarayya.
Kwamishinan ayyuka, Alhaji Umar Dudaye ne ya bayyana haka a ranar Talatar nan yayin taron tattaunawa da kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) ta shirya.
Ya ce za a kashe Naira biliyan 10.8 wanda ke wakiltar kashi 60 na kudaden da aka dawo da su wajen gina tituna domin inganta sufuri da saukaka zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka a jihar.
Dudaye ya ce ma’aikatar ta kammala ayyukan titina da magudanan ruwa guda 15, wanda ya kai kimanin kilomita 50 a fadin kananan hukumomi tara daga shekarar 2019 zuwa 2022.
Kwamishinan, ya ce wasu hanyoyi guda biyar da ke da nisan kilomita 90 ana kan gina su.
Kwamishinan ya lissafa hanyoyin da suka hada da Bulanguwa-Kumagannam kilomita 30, Danchuwa-Garin Bingel mai kilomita 18 da NTA Potiskum-Gujba kilomita 5.7.
Sauran sun hada da titin Buni Yadi kilomita hudu, titin garin Nguru kilomita 3.7, titin garin Potiskum kilomita 2.7, titin Obasanjo-Mallamatari-Gujbmai kilomita 2.5, titin garin Jaji-Maji mai tsawon kilomita 2.5, da dai sauransu.
Dudaye ya ce an kammala gada biyu na masu tafiya a kafa a Kasuwar Zamani ta Damaturu da Kasuwar Shanu ta Damaturu, yayin da wasu uku ke kan aikin a kasuwannin Nguru, Gashua da Potiskum.
Kwamishinan ya ce ma’aikatar ta gyara gadar Katarko da ta lalace, inda ya ce za ta gyara hanyoyin Kaliyari da Jajere da ambaliyar ruwa ta lalata. (NAN)