Connect with us

Kasuwanci

Kano: Hukumar CPC ta cafke matattun dabbobi a mayanka

Hukumar kare haƙƙin masu saye da masu sayar da kayayyaki ta Jihar Kano CPC, ta ce ta kama wasu matattun dabbobi a mayankar dabbobi ta Unguwa uku Ƴan Awaki da ke yankin ƙaramar hukumar Tarauni.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Musbahu Yakasai ya fitar a daren Litinin ɗin makon nan.

Sanarwar ta ce, Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan harkokin tabbatar da ingancin kayayyakin masarufi Alhaji Salisu Muhammad ne ya wakilci mai riƙon shugabancin hukumar Baffa Babba-Dan’agundi, wajen kamen.

Ya ce, hukumar ta samu labarin dabbobin ne da misalin karfe 6:00 na safiya.

“Mun samu labari daga wasu mutane masu kishi cewa an kawo matattun dabbobi a mayankar da suka hada da raguna da awaki bayan an yanka su a wani wuri.

“Nan take tawagarmu ta dauki mataki tare da kame dabbobin a kokarin mu na kare mutanen Kano daga amfani da kayayyakin na jabu da lalatattun kayayyaki.”

Adan haka ya yi nuni da cewa hukumar ta gayyaci wani Likitan Dabbobi domin gwada dabbobin ko sun dace da cin naman tare da tabbatar da ko da gaske ne yawancinsu sun mutu kafin a yanka su.

Haka kuma ya ƙara da cewa “Za mu yi maganin masu laifin yadda ya kamata.”

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa mai Babba-Dan’agundi ya buƙaci mahauta da su daina aikata irin wannan mummunar ta’ada ko kuma su fuskanci fushin mahukunta.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet