A Litinin ɗin makon nan ne Lauyan da ke kare gwamnatin tarayya, Ames Igwe, ya roƙi kotun da ta tilasta wa ASUU wajen komawa bakin aiki duba da illar da yajin aikin ke haifarwa.
Haka kuma Igwe ya ƙara da cewa la’akari da dokokin ma’aikata, kotun tana da ikon tilasatwa ASUU komawa bakin aiki.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Sai dai lauya mai kare kungiyar ta ASUU, Femi Falana, ya ce, wajibi ne gwamnatin tarraya ta fara bayyana illar da yajin aikin ya haifar kafin kotun ta tilasta komawa bakin aiki.
Da yake yanke hukuncin, mai shara’a Polycarp Hamman, ya ce yanke hukuncin ya zama dole domin batu ne na muradan ƙasa da kuma ƴancin da ɗalibai suke da shi na a basu ilimi kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin Najeriya.
