Labarai
Jam’iyyar PDP Ta Sanya Ranar Da Za Ta Sake Zaben Fidda Gwani a Zamfara

Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara ta sanya ranar Juma’a (gobe) domin sake gudanar da zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jihar.
A ranar Juma’ar da ta gabata, wata babbar kotun tarayya a jihar ta soke zaben fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar da Alhaji Dauda Lawal Dare wanda ya lashe zaben fidda gwanin.
To sai dai bisa dalilin saba ka’idojin kundin tsarin mulkin jam’iyyar na daga cikin dalilin da ya sanya kotun soke zaben, bayan tsohon dan majalisar tarayya Alhaji Ibrahim Shehu Gusau, ya roki kotu da ta soke zaben da ya ce yana cike da kura-kurai.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Ahmad Sani Kaura, ya ce an kammala shirya gudanar da zaben fidda gwani a jihar cikin kwanciyar hankali, inda ya kara da cewa za a samar da daidaito ga duk wanda ya tsaya takara.