Labarai
Mun cafke motoci fiye da 3,000 marasa lamba a Kano- FRSC

Hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta Najeriya FRSC shiyyar Kano, ta ce ta cafke fiye da motoci dubu uku wadanda ba su da lamba daga watan Agusta zuwa Satumba.
Shugaban hukumar Zubairu Mato ne ya bayyana hakan kamar yadda jaridar Solacebase ta ruwaito.
Ya ce, yi wa ababen hawa rijista na da matuƙar muhimmanci wajen inganta tsaro da daƙile aikata laifuka da sauran munanan ɗabi’u.
Shugaban ya ƙara da cewa, yanzu haka an samu raguwar hadurran kan tituna a jihar, domin a bana hukumar ta sami rahoton hadururruka 100 da doriya ne kadai, ba kamar bara ba da aka sami sama da 300.
Zubairu Mato ya danganta raguwar, ga tsauraran dabaru da hukumar FRSC ta jihar Kano ta kaddamar.
“Muna da motocin da ke kawar da kanana da manyan motocin dakon kaya da suka lalace a hanya domin kare duk wani cikas da ka iya faruwa a kowane lokaci.”
Sai dai ya nanata cewa, hukumar ta gudanar da wayar da kan jama’a a garejin motoci, da wuraren tarukan Jama’a a fadin masarautun Jihar guda biyar da kuma gangamin wayar da kan masu ababen hawa.
Kwamandan shiyar ya ce FRSC ta kafa kotunan tafi da gidanka domin dakile gudun wuce sa’a Akan tituna da yin lodin da ya wuce kuma da amfani da waya yayin tuki da duk wasu batutuwan da suka shafi karya dokokin hanya.
Dangane da batun ɗaukar matakin gaggawa kan haɗuran titina, Zubairu Mato ya bayyana cewa, hukumar na aiki ba dare ba rana domin bayar da agajin gaggawa ga wadanda hadari ya rutsa da su, da kuma kai su asibitin hukumar da ke Chiromawa, wanda ke ba da magani kyauta ga wadanda abin ya shafa.
Kwamandan na hukumar FRSC shiyyar Kano, ya kuma gargaɗi direbobi da su daina aikata laifukan da suka shafi tuki, kamar tuki cikin maye, da shan miyagun ƙwayoyi, da gudun wuce sa’a da kuma tuki ga wadanda suke ƙasa da shekaru 18, da yin waya yayin tuƙi.