Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a yau Alhamis.
Ya ce, bayan tuntuɓar abokan harkokin siyasa da magoya baya da abokan arziki,
“Na yanke shawara ba zan ɗaukaka ƙara ba a bisa hukuncin, na karɓi kaddara”.
Haka kuma ta cikin sanarwar shugaban majalisar dattawan, ya miƙa godiyarsa ga shugabannin jam’iyyar APC a jihar Yobe har ma da al’ummar mazabarsa da ya ke wakilta.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan hukuncin kotun da ta tabbatar da cewa ba shi ne ɗan takara ba.
