Connect with us

Labarai

Atiku Da Wike Sun Sake Wata Ganawa Ta Sirri A Birnin Tarayya

A ci gaba da kokarin sasanta rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya sake ganawa da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.

Wata majiya mai tushe a wajen taron ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa wasu manyan hadiman biyu sun halarci taron.

Ziyarar ta gudana ne a masaukin Gwamnonin Rivera a Asokoro da ke Abuja da yammacin ranar Alhamis din nan.

Majiyar ta ce da yawa daga cikin wadanda suka bi Atiku wajen taron ba su ji dadin yadda Wike ya tunkari Atiku kan wasu batutuwan da suka haddasa rikicin jam’iyyar ba.

Majiyar wadda ba ta so a ambaci sunanta ba saboda ba shi da izinin yin magana, ta ce Atiku wanda ya bude tattaunawar ya bukaci Wike da ya dawo su hada kai don magance matsalolin.

Ya ce dan takarar shugaban kasar ya roki Wike cewa ‘yan Najeriya na bukatar jam’iyyar PDP ta lashe zaben 2023 tare da bayyana dalilan da zai sa Wike ya kawo karshen rikicin.

Majiyar ta ce: “Amma mun yi mamakin yadda Wike ya mayar da martani. Gwamnan ya tunatar da Atiku game da taron da suka yi a Landan da kuma yarjejeniyar da aka cimma. Alkawarin da Atiku ya yi na cewa zai yi magana da shugaban jam’iyyar na kasa Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus.

“Alkawarin cewa shi (Atiku) zai dawo gare su bayan mako guda da kuma yadda bai kira su ba tun wancan lokacin.

Jigon ya kuma ce, a cewar Wike, mambobin BoT sun amince Ayu ya sauka, amma wasu suna rokonsa da kada ya yi murabus.

Sai dai kuma bayan sauraron Atiku, Wike ya yi alkawarin komawa ga jama’arsa, ya tattauna da su kan sakamakon taron kafin ya yanke shawara.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet