Featured
Man City ta yi wa Man United luguden kwallaye a Premier

Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Manchester City ta doke Manchester United da ci 6-3 a wasan mako na takwas a gasar Premier League da suka ƙara ranar Lahadi a Etihad.
Tun kafin hutun rabin lokaci Manchester City ta ci kwallaye 4-0 ta hannun Phil Foden da Erling Haaland kowanne ya ci bibiyu.
Bayan da suka huta suka koma karawar zagaye na biyu Foden da Haaland kowanne ya kara zura kwallo a raga.
Sai dai United ta zare uku ta hannun Dos Santos, sannan Anthony Martial ya zura biyu a raga daya daga ciki a bugun fenariti.
Da wannan sakamakon Manchester City tana mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 20, United kuwa tana nan da makinta 12 tana ta shida a teburin wasannin bana.
Manchester City ta yi nasara karo uku a jere a kan United tun bayan doke ta hudu da ta yi tsakanin Afirilun 2013 zuwa Nuwambar 2014.
United ta yi rashin nasara karo na 18 a Premier League a hannun City.
Liverpool da Chelsea sun yi nasara a kan United irin haka a babbar gasar tamaula ta Ingila.