Kasuwanci
Shugaban Kasa Zai Gabatar Da Kasafin Kudin 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 na Naira Tiriliyan 19.76 a gaban zauren majalisar dokokin kasar a ranar Juma’a.
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban kasa ya aikewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kuma aka karanta a zaman zaman majalisar na ranar Talata.
A cewar wasikar, za a gabatar da kasafin ne da misalin karfe 10:00 na safe a zauren majalisar wakilai na wucin gadi.
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce an yi shirye-shiryen karbar dukkan ‘yan majalisar dokokin kasar da kuma tawagar shugaban kasa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana gudanar da gyare-gyare a majalisar dattawa da ta wakilai, lamarin da ya sa ‘yan majalisar tarayya suka koma zauren majalisar na wucin gadi.