Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU Kishiyoyi

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta karya matsayin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) a lokacin da ta yi wa kungiyoyin biyu rijista a tsarin jami’o’in.

Kungiyoyin sun hada da National Association of Medical and Dental Academics (NAMDA) da Congress of Nigerian University Academics (CONUA).

CONUA kungiya ce ta malaman jami’o’in kasar nan kuma wani malami ne a jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife, Niyi Sunmonu ke jagoranta. An kafa kungiyar a cikin 2018 a OAU.

Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya bayyana cewa kungiyoyin biyu za su kasance tare da ASUU.

Sannan ya bayyana cewa kungiyoyin biyu za su ci gajiyar hakki da kuma gata da aka bai wa sauran kungiyoyin ilimi a fannin ilimin manyan makarantu.

Ba a dai san ko mene ne illar amincewa da kungiyoyin zai kasance kan ayyukan masana’antu na tsawon watanni bakwai da ASUU ta dauka ba.

ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu.

A cikin watan Agusta, kungiyar ta ayyana tsawaita yajin aikin na “sai baba ta gani kuma mara iyaka” na ayyukanta na Jami’o’i, tare da lura da cewa gwamnati ta kasa biyan bukatunta.

Masanan na neman ingantacciyar walwala, farfado da jami’o’in gwamnati da cin gashin kansu na ilimi da dai sauran bukatu.

Wani kashin da ke damun malaman shi ne rashin biyan kudaden farfado da jami’o’in, wanda ya kai kimanin naira tiriliyan 1.1.

Sai dai gwamnatin tarayya ta ce ba ta da kudin da za ta biya irin wannan adadin, saboda karancin man fetur a zamanin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet