Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Gargadi Masu Bin Hanyar Lokoja Zuwa Abuja

Gwamnatin Tarayya ta gargadi masu ababen hawa da ke tafiya Arewa daga Kudu da Gabashin kasar nan ta Jihar Kogi da su guji hanyar Lokoja zuwa Abuja.
Kwanturolan ayyuka na gwamnatin tarayya a jihar Kogi, Engr Jimoh Kajogbola ne ya yi wannan gargadin a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja, inda ya gargadi masu ababen hawa da su zabi hanyar daban.
Ya ce, “Saboda ambaliyar ruwa da ake yi a kasar, kogin Neja ya mamaye titin motoci biyu daga Lokoja-Abuja a Koton-Karfe tare da sanya shi hadari ga masu amfani da hanyar.
“An shawarci masu ababen hawa da suka fito daga Kudu-maso-Yamma zuwa Abuja su wuce hanyar Ilorin zuwa Mokwa-Bida, yayin da masu ababen hawa daga Gabas da Kudu-maso-Kudu ake shawartar su wuce ta hanyar Makurdi-Lafia.”
Madadin hanyoyin, a cewarsa, yakamata a kiyaye har zuwa lokacin da ruwan zai koma.