Labarai
Gobara Ta Tashi A Ginin Majalisar Dokokin Jihar Kogi

Gobara a ranar Litinin ta kone zauren majalisar dokokin jihar Kogi.
Duk da haka, ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Sai da jami’an kashe gobara na rukunin Dangote sun shiga tsakani suka yi ta fama da gobarar na tsawon sa’o’i biyu, wanda hakan ya hana gobarar tashi zuwa zauren majalisar baki daya.
Da yake magana da gidan Talabijin na Channels, daya daga cikin jami’an tsaro a Majalisar ya ce gobarar ta tashi ne da tsakar dare, amma an ga gobara da misalin karfe 7 na safiyar ranar Litinin.