Connect with us

Tsaro

Jami’an KAROTA sun cafke direban Adaidaita Sahu ɗan damfara

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta ce, ta cafke wani magidanci ɗan damfara bayan ya damfari wata kuɗi naira dubu ɗari shida N600.000

Hakan na ƙunshe ne ta wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Malam Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar a daren yau Talata.

Sanarwar ta ce, Jami’an hukumar ta KAROTA, sun sami nasarar kama magidancin ne mai suna John Bandes a kan titin Obasanjo da ke cikin birnin Kano.

“A makon da ya gabata ne wata budurwa mai suna Jenifer Paul ta shigar da ƙorafi a Hukumar KAROTA bayan Damfarar da magidancin ya yi mata ta hanyar amfani da babur ɗin Adaidaita Sahu” inji sanarwar.

Haka kuma Nabilusi a sanarwar ya ƙara da cewa, Jenifer ta shaida wa hukumar cewa lokacin da ta hau Adaidaita Sahun watanni biyu da suka gabata, magidancin ya damfareta zunzurutun kudi har naira dubu ɗari shida.

An samu nasarar cafke Adaidaita Sahun mai lambar RRN 231QA da kuma Koriyar lambar FGE 19-0849.

Magidancin mai suna John Bandes ɗan kimanin shekaru 45 ya bayyana wa Humar KAROTA ba shi kadai yake aikata Damfarar ba suna da yawa, kuma sun shafe fiye da wata shida suna Damfarar jama’a a nan Kano da babban birnin tarayyar Abuja.

“A binciken da hukumar KAROTA ta gudanar ta gano yadda John ke amfani da wani sinadari a cikin wata kwalba, da zarar sun zubawa fasinja zai sami juyewar Kai, sai yadda suka yi da shi kamar yadda Janifer ta bayyana” a cewar sanarwar.

Haka kuma ya ce, KAROTA ta GANO cewa John ya jima yana aikata saƙa a mugun zare kafin dubunsu ta cika.

“Wani binciken sirri da KAROTA ta samu ya bayyana cewa fiye da watanni shida da suka gabata Rundunar ‘Yansanda ta baza koma wajen ganin an damke John ɗin sai a wannan rana dubunsu ta cika, inji Jami’n.

Sanarwar ta hukumar KAROTA ta kuma ce, Hukumar ta miƙa John ga Baturen ƴan sanda na Badawa domin faɗaɗa bincike tare da ɗaukar mataki na gaba a kansa.

Haka zalika kukumar KAROTA ta ja hankalin jama’a da su ci gaba da sanya ido a kan duk wani matuƙin Adaidaita Sahu kafin su hau domin gujewa faɗawa hannun ɓata-gari.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet