Labarai
Tinubu Da Jiga-jigan Jam’iyyar APC Sun Gana Kan Kwamitin Yakin Neman Zabe

Gwamnoni da ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu a halin yanzu suna ganawa a otal din Transcorps Hilton da ke Abuja.
Babban jigo na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu da Shettima na cikin taron.
Majiyoyi sun shaida wa Jaridar Daily Trust cewa za a tattauna batun kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar da kuma lokacin da jam’iyyar za ta fara yakin neman zaben ta a taron.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, jinkirin fara yakin neman zaben jam’iyyar APC ya samo asali ne sakamakon rikicin da ke tsakaninta da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa yayin da masu ruwa da tsaki ke gudanar da taruka daban-daban.
A daya daga cikin tarurrukan da wasu gwamnonin APC da kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta, shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce jam’iyyar za ta yi rashin nasara a zaben 2023 ba tare da sa hannun gwamnonin ta ba.
Kafin bude yakin neman zaben da INEC ta yi, sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, James Faleke, ya fitar da jerin sunayen mutane 422 na kwamitin.
Sai dai ci gaban ya haifar da rikici tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da suka hada da kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da gwamnonin da ke cikin jam’iyyar, saboda a cewarsu ba sa cikin shirin.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, An ce wasu gwamnonin sun fusata ne saboda ba a saka sunayen wadanda suka zaba a cikin kwamitin yakin neman zaben ba.
A ci gaba da takun-saka da aka yi a cikin jerin sunayen, babban daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya sanar da dage taron nasu domin share fagen shigar da karin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.
Sai dai kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo (SAN) ya shaida wa wakilinmu a jiya cewa za a fitar da jerin sunayen karshe a cikin wannan mako, inda daga nan ne za a fara gudanar da yakin neman zabe a hukumance.