Labarai
Yobe: Sojoji sun cafke Tabar Wiwi ta kusan Miliyan 50

Rundunar haɗin gwiwa ta sojin Najeriya shiyyar yankin Arewa maso Gabas da ke birnin Damaturu a jihar Yobe, ta damƙa ƙunshin tabar wiwi Casa’in da Takwas da kuɗinsu ya kai naira miliyan huɗu da dubu ɗari tara ga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA.
Kwamandan sashen, Manjo Janar Koko Isoni ne ya bayyana hakan yayin da ya ke miƙa wa hukumar Tabar da ya ce an cafke ta ne ranar Litinin ɗin makon nan a birnin Damaturu.
Kwamandan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Birgediya Janar Umar Mu’azu, ya ce dakarun bataliya ta 159 da ke Ƙaramar Hukumar Geidam ne su ka kama kayan a ranar 7 ga watan Oktoban 2022.
“Mai dakon kayan ya watsar da su, ciki har da motar da ke ɗauke da kayan lokacin da ya ga tawagar sintiri,” in ji shi.
A nasa jawabin, kwamandan NDLEA na jihar, Aliyu Yahaya, ya yabawa rundunar sojin bisa wannan kwazo, inda ya kara da cewa kowanne kunshi na tabar ya kai N50,000.
Yahaya wanda ya samu wakilcin mataimakin kwamandan jihar, Ogar Peter, ya yaba da hadin kai tsakanin hukumomin tsaro a jihar.
“Mun yi farin cikin samun wannan nasara. Wannan karimcin ya nuna hadin kai da ke tsakanin jami’an tsaro a jihar,”
in ji shi, ya kara da cewa rundunar sojin Najeriya ta dukufa wajen dakile safarar miyagun kwayoyi a jihar.