Connect with us

Featured

Salah ya kafa tarihin cin kwallaye 3 cikin sauri a gasar zakarun Turai

Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa

 

Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya kafa tarihin shiga sahun wadanda suka yi nasarar zura kwallaye 3 a wasa guda cikin sauri a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da ya zura kwallayen 3 wato hattrick cikin mintuna 6 da shiga fili a karawarsu da Rangers daren jiya Laraba.

Kwallayen na Salah dai ya goge tarihin Bafetimbo Gomis na Lyon wanda ya taba nasarar zura kwallaye 3 cikin mintuna 8 yayin wasansu da Dinamo Zagreb a 2011 karkashin makamanciyar gasar.

Yayin wasan na jiya da ya gudana a Ibrox Liverpool ta tashi wasa 7 da 1 ne tsakaninta da Rangers har gidanta kuma shi ne wasa na farko a cikin kakar nan da aka ga ‘yan wasan Liverpool na nuna bajinta irin wannan.

Har zuwa yanzu dai wasanni 4 kacal cikin 11 da Liverpool ta doka ne ta samu nasara, musamman a gasar firimiyar Ingila da yanzu haka kungiyar ke matsayin ta 10 da maki 10, dalilin da ke ci gaba da janyowa ‘yan wasan kakkausar suka daga magoya baya.

Tuni dai wasu masu sharhin wasanni suka fara shawartar kungiyar kan ta fara ajje Salah a benci yayinda wasu ke ganin kamata ya yi a rage albashin Vigil van Dijk wanda ya gaza katabus a wannan kaka, kuma ko a wasan na jiya Salah yana benci ne aka sauya shi inda ya samu nasarar zura kwallayen 3.

A bangaren Rangers wadda ke dawowa gasar ta cin kofin zakarun Turai karon farko bayan shekaru 12 har zuwa yanzu bata da maki ko guda yayinda ta sha ruwan kwallaye 16 inda mai horar da kungiyar Van Bronckhorst ke cewa mintunan wasan na jiya ya zame musu tamkar kwana da yini.

Sai dai duk da nasarar ta Liverpool kungiyar ta ci gaba da zama ta 2 a rukuninta, yayinda ta ke bukatar akalla canjaras da Ajax gabanin iya tsallakawa rukuni na gaba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet