Connect with us

Labarai

Gwamnan Rivers Ya Zargi Shugaban Jam’iyyar PDP Da Karbar Kudade A Hannun Wani Gwamna

 

 

Nyesom Wike ya zargi shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu da karbar Naira miliyan 100 daga hannun wani gwamna.

Gwamnan jihar Ribas ya yi wannan zargin ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’ar nan a Fatakwal inda ya kuma yi barazanar bayyana karin wani abun “idan aka kai shi bango”.

“Bari in gaya muku, Ayu ya karbi Naira miliyan 100 daga hannun gwamna,” in ji shi, yana mai jaddada cewa jigon PDP ba zai iya musanta zargin ba.

“Ina gaya muku wani gwamna. Bari shi (Ayu) ya ce a’a ba gaskiya ba ne kuma zan gaya maka wane gwamnan. Waɗannan abubuwa ne da mutane ba su sani ba, ”in ji Wike.

“Idan ba don soyayyar wannan jam’iyyar ba, idan muka saki abin da muke da shi, ‘ya’yan Ayu za su gaya masa cewa ‘Ba ka zama babanmu ba.”

A cewar Wike, ba ya tsoron shugaban jam’iyyar, yana mai cewa Ayu ba zai iya yin tasiri ga al’ummar jihar Ribas a kan wadanda za su kada kuri’a a babban zaben shekara mai zuwa ba.

“Ba shi da ikon yin hakan,” in ji shi. “To me yasa zan ji tsoronsa?”

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Wike ya ci gaba da cewa ya kamata Ayu ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar PDP, yana mai cewa jigon jam’iyyar ya yi alkawarin cewa zai yi hakan idan dan takarar shugaban kasa ya fito daga arewa (yanki daya da Ayu).

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet