Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna Za Ta Gina Dam A Dazuzzukan Jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta kammala shirye-shiryen gina madatsar ruwa a dazuzzukan da suka kai hekta 800,000 da ke tsakanin garuruwan Buruku da Birnin-Gwari, wanda a tsawon shekarun da suka gabata, sun kasance mafakar ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.

Babban darakta na Hukumar Tsare-tsare da raya birane ta Jihar Kaduna, Ismail Umaru-Dikko ne, ya bayyana haka a taron gabatar da zuba jari na Kaduna karo na 7 da ake gudanarwa.

A cewar shugaban KASUPDA, aikin dam din ba wai kawai zai magance matsalolin tsaro a jihar ba, har ma zai kawo karshen ambaliyar ruwa a cikin babban birnin Kaduna.

Ya ce, “Daga Buruku zuwa Birnin-Gwari da muke fama da fashi da makami tun a tarihi, ya koma wurin satar shanu da kuma yin garkuwa da mutane da fashi.

“Don haka, muna jin cewa dole ne wani abu ya faru a can. Muna da kasa mai girman gaske wadda ba a taba amfani da ita a wurin ba, shi ya sa ba za mu iya nade hannayenmu kawai mu kyale masu laifi su ci gaba da cin gajiyar wannan kasa mai albarka ba.

“Saboda haka, mun fito da tsarin, muka gano cewa daga Buruku zuwa Birnin-Gwari, muna da fili kusan hekta 800,000 wanda kusan jihohi biyu ne a wani sashe na kasar nan. Muna ƙirƙirar dam a can.

“A halin yanzu, Kaduna kamar magudanar ruwa ce, wanda ke fitowa daga Bauchi, ya bi ta nan zuwa Dam din Shiroro. Ruwan wani lokaci yana haifar da ambaliya a nan. Don haka, a matsayin hanyar samar da mafita mai ɗorewa, za mu gina madatsar ruwa, mu tanadi ruwa, mu magance matsalar ambaliyar ruwa da kuma amfani da ruwan a lokacin rani don noman ban ruwa.

“Wannan mun yi imanin zai kuma samar da ayyukan yi, mafi yawan matasan da ke gaggawar karatun harkokin kasuwanci da lissafin kudi a jami’o’i za su iya shiga harkar noma.

“Za mu karfafa wa matasa gwiwa kan harkar noma, shi ya sa muka kawo takin OCP domin hada hannu da gwamnati a wannan fanni. Mun kuma kawo bankin NEXIM domin mu ga yadda za mu iya fitar da kayan amfanin gona daga nan gaba daya.”

A halin da ake ciki kuma, gwamnatin jihar Kaduna ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kungiyar ‘yan kasuwa da ma’adanai da noma ta Kaduna domin kafa kauyen fina-finai a cikin kasuwar baje kolin kasuwanci ta Kaduna.

Da yake magana kan shirin Film Village, Shugaban Hukumar Babban Birnin Kaduna, Hafiz Bayero, ya ce hadin gwiwar ba za ta gina sabbin gine-gine ba ne, sai dai a yi amfani da tsofaffin gine-ginen kasuwar baje kolin wadanda a halin yanzu ba a yi amfani da su ba don sake mayar da hankali a kansu.

Ya kara da cewa “Muna neman samun fili a cikin hadaddiyar kasuwar baje kolin, inda mutane za su iya zuwa su yi fina-finai kafin su fito da kuma bayan fitowar su da kuma tura fim din zuwa kasuwar fina-finai ta duniya,” in ji shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet