Labarai
Gwamnatin Zamfara ta rufe kafofin da suka yaɗa labaran jam’iyyar PDP

Gwamnatin jihar zamfara ta rufe wasu kafafen yaɗa labarai mallakin gwamnatin tarayya da masu zaman kansu a jihar, saboda yaɗa labaran al’amuran da suka shafi harkokin jam’iyyar adawa ta PDP.
Majiyar Kakaki Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin ta umarci kwamishinan ƴan sandan jihar da ya kama duk ƴan jaridun da suka halarci taron.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Malam Ibrahim Magaji Dosara ne ya sanar da hakan ta gidan rediyon karamar hukumar.
Umarnin ya shafi Radio Nigeria Pride FM da NTA Gusau da kuma Gamji FM da dai sauransu.