Wasanni
Ina da tabbacin Barcelona za ta dauki kofi a bana – Xavi

Mai horas da kungiyar Barcelona Xavi Hernandes ya ce har yanzu suna nan kan bakar su na lashe gasa a kakar bana, duk da rashin nasarar da suka yi a hannun Inter Milan a gasar zakarun Turai da kuma na ranar Lahadi a Santiago Bernabeu a hannun Real Madrid.
A zantawar sa da manema labarai gabanin wasan su da Villarreal a ranar Alhamis din nan ya ce sun gina tawagar ne don samun nasarar lashe gasa, duk da a wannan makon ya fuskanci suka mai tsauri.
Ya ce a yanzu ya maida hankali ne wajen ganin tawagar ta sa, ta sake farfadowa don dorawa daga inda suka tsaya.
Xavi ya kuma yabawa kokarin Real Madrid wajen dakile duk wasu hare-haren da suka kai yayin wasan El-Clasico.
Rashin nasarar Barcelona a wasan su da Real Madrid dai ya sanya ta komawa mataki na biyu a teburin La liga sannan kuma kunnen dokin da ta yi da Inter Milan a gasar zakarun Turai komawa mataki na uku a rukunin su, lamarin da ake ganin kungiyar na iya komawa buga gasar Europa.