Labarai
Sojoji sun sake ceto ƴan makarantar Chibok 2 da ƙarin mutane 99

Rundunar sojin Najeriya ta ce, dakarunta sun samu nasarar ceto ƙarin ƴan matan makarantar sakandaren Chibok da ƴan Boko Haram suka sace su biyu da ƴaƴa shida da suka haifa tare da ƙarin wasu mutane casa’in da tara.
Babban kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation Haɗin Kai Manjo Janar Waidi Shaibu ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai rundunar ta gudanar Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Ya ce, dakarun sun samu nasarar kuɓutar da mutanen ne a sassa daban-daban na jihar ta Borno a sansanonin ƴan ƙungiyar Boko Haram.
Haka kuma kwamandan ya ƙara da cewa cikin sauran mutane casa’in da taran da aka kuɓutar ɗin akwai mata arba’in da bakwai da kuma maza hamsin da biyu.