Connect with us

Featured

Bola Tinubu Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 100 A Kano

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano.

Tinubu wanda ya kai ziyarar kwanaki 2 a Kano, ya bayar da gudunmawar ne a lokacin liyafar cin abinci da kungiyar ‘yan kasuwa ta Kano ta shirya masa domin karrama shi.

Ya ce sun bayar da tallafin ne domin taimakawa da rage radadin ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Jaridar Kakaki Hausa ta ruwaito hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ta bayyana cewa an samu ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 19 cikin 44 na jihar inda mutane 23 suka mutu, 106 suka jikkata, sannan gidaje 12,919 suka lalace yayin da gonaki 14, 496 suka lalace a kananan hukumomin biyar.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya yi alkawarin sake mayar da masana’antun da ake da su tare da mayar da su a matsayin tushen ci gaban masana’antu da bunkasa ba kawai ga Arewa ko Kano ba har ma da kasa baki daya.

Ya kuma yabawa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa kokarinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar, inda ya bayyana gwamnan a matsayin “aboki kuma amintaccen abokin tarayya”.

Ya kuma yi wa ’yan kasuwar alkawarin cewa zai samar da yanayin da zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.

Masu jawabai a cikin ‘yan kasuwar sun gabatar da tsarinsu ga Tinubu, inda suka yi kira gare shi da ya mai da hankali kan wutar lantarki saboda an rufe masana’antu da yawa saboda rashin isasshen wutar lantarki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet