Labarai
Wani Hatsarin Mota Yayi Sanadiyyar Rasa Ran Mutane Biyar

Fasinjoji 5 ne suka rasa rayukansu a kan hanyar Kaduna zuwa Kachia a lokacin da motar bas din da suke tafiya a ciki ta direban ya kasa sarrafara, kuma ta afkawa wani tirken wutar lantarki.
A cewar Mista Joseph Amos, daya daga cikin fasinjojin da suka tsira a halin yanzu ya ce, suna karbar magani a wani asibiti, dake Kaduna, “mun hau motar bas daga Kaduna zuwa Kafachan. Mu takwas ne a cikin bas ɗin, ba zato ba tsammani, bas ɗin ta kwace kuma ta afkawa wani tirke . Mutane biyar ne suka mutu nan take.”
Ya ce yayin da direban ke gudun wuce kima, sai suka gargade shi a kan cewa, hanyar bata da kyau, kwana da wasu ramuka, amma bai saurare su ba.
Rahotanni sun kuma nuna cewa, An kai wadanda suka mutun zuwa dakin ajiyar gawarwaki.