Featured
Mai martaba Sarkin Kano yayi sabbin nade nade a fadarsa

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR ya naɗa Alhaji Bashir Mahe Bashir Wali a matsayin sabon walin kano da Dakta Mansur Mukhtar Adnan a matsayin sabon Sarkin Ban Kano ɗaya daga cikin masu zabar Sarkin Kano.
Anyi naɗin ne a cikin fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a yau juma’a.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan naɗin, Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace ya naɗa Dakta Mansur Mukhtar Adnan saboda gogewar sa da irin aikace aikacen da yake gudanar a gwamnati.
Ya kuma hori sabin hakiman da su bayar da gudumawar da ta dace wajan munkasa rayuwar alummar masarautar Kano.
Sabbin hakiman sun nuna farin cikin su da zabin su da Mai Martaba Sarkin Kano yayi musu kuma ya nada su a matsayin hakiman da zasu bayar da gudumawa a masarautar kano.
Wakilin Gwamnan jihar Kano, Mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna da Ministoci da ƴan majalisun tarayya da na jahoji sun halarci bikin nadin.