Amira Souleyy daga garin Maraɗi na jamhuriyar Nijar ita ce ta rubuta labari mai taken ‘Gudun Gara‘.
BBC ta wallafa a shafinta cewa, Ksancewar labarinta ne ya zo na ɗaya a gasar, ta samu kyautar kuɗi har dalar Amurka dubu biyu.
Sai kuma Hassan Labaran Dan Larabawa da ta zo ta biyu wadda ita kuma ta samu kyautar Dala dubu ɗaya da ɗari biyar.
Maryam Muhammad Sani, ƴar asalin jihar Kano ce ta zo ta uku a gasar inda ita ma ta samu kyautar Dala dubu ɗaya.
