Labarai
Hukumar NEMA Ta Raba Kayan Tallafin Magunguna A Wasu Asibitocin Kano

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA a ranar Larabar da ta gabata ta bayar da tallafin magunguna da kayayyakin masarufi ga wasu asibitoci uku da ke jihar Kano domin tallafawa mutanen da bala’oi daban-daban ya shafa a jihar.
Babban Daraktan NEMA, Mustapha Habib, a lokacin da yake gabatar da kayayyakin, ya ce tallafin na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na tallafa wa mutanen da fashewar iskar gas da sauran bala’o’i suka shafa.
Shugaban wanda ya samu wakilcin ko-odinetan yankin Kano da Jigawa Dr Nuraddeen Abdullahi ya ce tun da farko hukumar ta yi alkawarin tallafa wa asibitocin guda uku don taimakawa mutanen da fashewar ta shafa.
Asibitocin sun hada da asibitin kwararru na Murtala Muhammad (MMSH), cibiyar kula da lafiya matakin farko ta Ja’en da kuma cibiyar kula da lafiya ta Sharada.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka bayar sun hada da katan 10 na IV Fusion, Saline na kashi 5 bisa 100 na al’ada,sinadarin wanke hannu, sinadarin mentholated, katan 50 na allurar hydrocortisone da safar hannu na tiyata da dai sauransu.
Da yake jawabi tun da farko, kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Tsanyawa, ya ce tallafin zai taimaka wajen inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.
Tsanyawa, wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta Kano, Amina Aliyu Musa, ya yabawa hukumar NEMA bisa wannan tallafin, musamman ga asibitin kwararru na Murtala Muhammad, wanda ake amfani da shi wajen kai dauki ga kusan dukkan wadanda suka kamu da cutar a jihar.
“Gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 15 wajen sayan magunguna da kayayyakin masarufi ga wadanda bala’in Sharada ya rutsa da su a asibitocin uku, wadanda ke ba da ayyukan kiwon lafiya na gaggawa,” in ji shi.