Shugaban hukumar na ƙasa Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ne ya bayyana hakan yayin da yake kare kasafin kuɗin hukumar gaban kwamitin kula da miyagun kwayoyi na majalisar wakilai.
Ya ce, jami’an hukumar sun samu wannan nasara ne a tsakanin watan Janairun bara zuwa watan Satumban bana.
Buba Marwa, ya ƙara da cewa, hukumar ta kuma cafke masu tu’ammali da miyagun ƙwayoyi mutum dubu goma sha tara da ɗari uku da arba’in da ɗaya tare da masu safarar ƙwayoyi su ashirin da biyar akwas.