Labarai
Ƴan sanda sun saki tunkiyar da su ka tsare bisa zargin cinye soyayyen kifi

Rundunar ƴan sanda jihar Borno ta saki wata tunkiya da aka kama bisa zargin ta da cinye soyayyen kifi da wani Malam Yusuf Ibrahim ke sayar wa a unguwar Bulabulin a Maiduguri babban birnin jihar.
Jaridar Zagazola Makama ta ruwaito cewa ran Malam Ibrahim ya ɓaci ranar Asabar ɗin da ta gabata baya da tunkiyar ta faki idanunsa ta daka wa kifin wawa ta kuma tsere.
Mai kifin ya yi ƙorafin cewa watanni biyar kenan tunkiyar mallakar wata mata mai suna Luba Mohammed, tana cinye masa kayan sana’ar sa, shi ne ya nemi ƴan sanda da su kamo ta domin hukunci.
Mai sayar da kifin ya koka da kakkausar murya kan cewa tunkiyar da ke unguwarsu ɗaya, ta haifar masa da asara har jarin sa ma na shirin karye wa.
Sai dai bayan da tunkiya ta kai wa kifinsa hari a ranar Asabar, daga karshe ya yanke shawarar shigar da ‘yan sanda.
Daga baya ‘yan sanda sun kama tunkiya kuma suka tsare ta cikin dare.
Daga bisani hedikwatar ‘yan sanda ta Bulabulin ta sake shi a ranar Lahadi bayan da Ibrahim ya sasanta da mai tunkiyar.
Daga karshe dai Ibrahim ya hakura ne bayan da manyan unguwa su ka haɗu su ka ba shi hakuri, inda duk da haka sai da ya shinfida sharuɗɗan cewa idan ta kuma to zai shigar da kara.