Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Dawowar Zirga-zirgar Jirgin Kasan Kaduna-Abuja

Gwamnatin tarayya a ranar Litinin din nan ta ce aikin jirgin kasa na layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna zai dawo cikin wannan wata na Nuwamba.
Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ba da katin shaida na ma’aikatar sa a Abuja.
Ya ce an samar da isasshen tsaro domin tabbatar da lafiyar fasinjoji. Sai dai Ministan bai bayar da takamaiman ranar da za a ci gaba da aikin ba.
Sambo ya ce ma’aikatar ta koyi isassun darasi daga harin da aka kai a watan Maris wanda ya yi sanadin mutuwar fasinjoji da dama da ya kai ga dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.